<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>99</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Akwai sunan nan mai daɗi wanda ba mai kamarsa,
 Wato sunan Ubangiji, begen dukan Masu Bi.

[V2]
 KORUS
 Sunan nan, Yesu ne, sunansa da daɗin ji,
 Sunan nan, Yesu ne, begen dukan Masu Bi.

[V3]
 2) Tun da na ji sunan Yesu, murna na ke yi sosai.
 Wurinsa na sami ceto, gafara da kwanciyar rai.
 Korus

[V4]
 3) Cikin sunan nan mai girma, a ke samun ceto fa,
 Cikinsa a ke sujada, cikinsa a ke addu'a.
 Korus

[V5]
 4) Sunan nan ya buɗe ƙofa, zuwa Allah Ubansa,
 Gama ban da sunan Yesu, Allah ba za ya ji mu ba.
 Korus</lyrics>
<title>Akwai Sunan Nan Mai Daɗi Wanda Ba Mai Kamarsa LW99</title>
</song>